Monthly Archives: June 2017

HUKUNCIN ZAKKAR FID- DA KAI

Category : ARTICLES , SALEH KAURA

“Zakkatul Fidir” ita ce ake kira a Hausance da “Zakkar Fid da kai”, ko “Zakkar kono”, ma’anarta kuma ita ce: zakkar da ta wajaba kowane Musulmi ya fitar da ita kafin gabatar da sallar Idi karama, kowa gwargwadon sa’i daya na abincin da aka fi amfani da shi a garin da yake, babu babba, babu yaro, ba namiji ba mace, babu da babu bawa; kowa sai ya fitar; Sayyiduna Abdullahi Ibn Umar (Allah ya kara yarda da su) ya ruwaito cewa: “Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa Alihi wa sallam) ya farlanta wa mutane bayar da zakkar fid da kai a watan Ramadhan, sa’i ne na dabino, ko na alkama, da ta wajaba akan kowane Musulmi, d’a ko bawa, namiji ko mace.” [al-Bukhari, 2/130; Muslim, 2/677].. kowa zai fitar wa wanda ciyar da shi ta wajaba akansa..

Amma sharadin bayar da ita shi ne ya zamana mutum yana mallakar sama da abin da yake bukata a ranar idi, saboda haka talakan da ba ya mallakan sama da abin da zai ci, shi da iyalansa a daren idi, wato daren da aka ga watan Shawwal, da kuma ranar idi, to kuwa lallai wannan ibada ta zakkar fid da kai, ba ta hau kansa ba, saboda ba zai iya ba, shi kuwa: ((Allah ba ya daura wa kowane rai wani abu sai abin da zai iya)) [al-Bakra: 286]..

Allah Madaukakin Sarki ya farlanta wannan zakka ne domin ta tsarkake mai Azumi daga kura-kuren da ya aikata a lokacin Azumi, irin su: alfasha a zance, da kuma ayyuka marasa fa’ida.. haka kuma Allah Madaukakin Sarki ya farlanta zakkar fid da kai ne; saboda a wadata mabukata, kada a bari har sai sun roki abin da za su ci a ranar idi, ranar da gaba dayan Musulmai suke cike da farin ciki da zuwansa, a dalilin haka ne ma Sayyiduna RasululLahi (SallalLahu alaiHi wa Alihi wa sallam) yake cewa: ((Ku hutar da su yawon nema a wannan rana)) [Dar Kutniy 2/152; al-Baihakiy, 4/175].

Game da lokacin da ake fitar da zakkar fid da kai kuwa, malamai sun kara wa juna sani, inda bayanansu game da haka ya zo kaman haka:

• Mazhabar Imam Abu Hanifah (Allah ya kara yarda da shi): ta tafi akan cewa za a fitar zakkar fid da kai ne da zaran alfijir din ranar idin karamar sallah ya fito.

• Mazhabar Imam as-Shafi’iy, da Mazhabar Imam Ahmad (Allah ya kara yarda da su): sun tafi akan cewa zakkar fid da kai tana wajaba ne da zaran rana ta fada a ranar karshe na watan Ramadhan..

• Mazhabar Imam Malik (Allah ya kara yarda da shi): su kuwa Malikawa suna ganin cewa ya halatta a fitar da zakkar fid da kai kafin ranar idi da kwana daya ko biyu; domin an ruwaito cewa Sayyiduna Abdullah bn Umar da Al-Hassan (Allah ya kara yarda da su) cewa babu laifi a fitar da wannan zakkar kafin ranar idi da kwana daya ko biyu…

Saboda haka sam babu laifi idan aka gaggauta bayar da zakkar tun kafin ranar idin da kwana daya ko biyu..

Sai dai fa idan lokacin bayar da wannan zakka ya wuce, to zakkar ba ta saraya, dole ne a bayar da ita a matsayin biyan bashi “Qadha’i”.

Ana bayar da wannan zakka ne ga talakawa, haka ma mutane takwas din da ake ba su zakka –kaman yanda ya zo a ayar Suratut Tauba- suna cikin wadanda za a bai wa wannan zakkar ta fid da kai, Allah Madaukakin Sarki yana cewa: ((Ita zakka ana bayar da ita ne ga talakawa fakirai, da talakawa miskinai, da masu aikin tattara ta, da kuma wadanda ake tarairayar zukatansu domin shiga Musulunci, da wurin ‘yanta bayi, da biyan bashin wanda bashi ya yi masu kanta, da mayaka masu daukaka kalmar Allah, da matafiya, wannan kam wajibi ne da ya zo daga Allah, lallai Allah shi ne cikakken masani, mai kuma yawan hikima)) [at-Tauba: 60].

Sai dai duk da haka, za a iya bai wa mutum daya, kaman yanda za a iya rarrabawa mutane sama da daya, abin dai da za a lura da shi kawai shi ne: hutar da mabukata da wahalar nema a wannan rana..

Kaman yanda muka bayyana a baya, ana fitar da zakkar fid da kai ne daga abincin da aka fi amfani da shi a garin da mutum yake, kaman mu ce: shinkafa, da masara, da dawa da sauransu, kowane mutum za a fitar masa da sa’i daya ne irin sa’in Sayyiduna RasululLah (SallalLahu alaiHi wa Alihi wa sallam), wanda ya yi daidai da (kilo giram 2.04); amma wanda ya bayar da abin da yafi haka, ya kyauta zai kuma sami lada akan hakan in Allah ya yarda.

Haka ma za a iya fitar da zakkar fid da kai da kudi, sai a kiyasta kudin abincin da za a fitar din a bai wa mabukata..

Allah ya amshi ibadunmu, ya kuma dawwamar mana da darasin da muka dauka a cikin wannan mata, ta yanda za mu cigaba da gabatar da ayyukan alhairi na ibada da na mu’amala a tsakaninmu, mu cigaba da kyautata wa juna, da kuma hararo kwarjinin Allah Madaukakin Sarki a dukan rayuwarmu, amin.

Saleh Kaura

28 Ramadhan, 1438

23 June, 2017


DURUSUL HASANIYYA, RAMADHAN 1438/2017

DARASIN: MAULANA IMAM DR. IBRAHIM AHMAD MAQARY (LIMAMIN BABBAN MASALLACIN KASA NA ABUJA) –HAFIZAHULLAH

A FADAR: MAI ALFARMA SARKI MUHAMMAD AS-SADIS, SARKIN MAROKO

Tarjama: Saleh Kaura

Gabatarwa: In Allah ya so zan gabatar da tarjamar wannan muhimmin darasi ne kadan-kadan, inda zan raba shi zuwa kashi biyar.. Allah ya dawo mana da Maulana Imam Dr. lafiya.. ga kashi na farkon:

Maulana Dr. I. A. Maqary ya ce:

BismilLahir Rahmanir Rahim.

Ina gode wa Allah, wanda shi ne ake gode wa da dukan harsuna, shi ne kuma aka sani da yawan baiwa gami da kyautatawa.. Shi ne ya halicci dan Adam, ya kuma sanar da shi hanyoyin bayyana abin da yake so..

Tsira da aminci su tabbata ga shugabanmu Muhammadu, wanda Allah ya zabe cikin daga cikin ‘ya’yan Adnan, tsira da amincin su hada da danginsa tsarkaka, da sahabbansa masu karamci a kowane lokaci dare da rana..

Ya shugabana mai girma, Amirul Muminina:

Darasin yau –idan kun bayar da izini- zai kasance ne akan “Dangantaka ta ruhi da ta al’adu cikin alakar da hada kasar Maroko da Najeriya, karkashin maganar Allah Madaukakin Sarki da take cewa: ((Ya ku Mutane, lallai mun halicce ku ne daga namiji da mace, sannan muka sanya kuka zamo al’ummomi da kabilu; saboda ku yi taimakekeniya da juna, ku sani cewa: wanda ya fi daraja a wurin Allah shi ne wanda ya fi tsoron Allah, lallai Allah mai cikakkiyar masaniya ne, kuma kwararre akan komai)) [al-Hujrat: 13].

Lallai akwai dangantaka ta imani da ta mutuntaka masu zurfi, kuma masu tarihi da suka hada tsakanin kasar Maroko da Najeriya.. dangantakar da take bukatar masu bincike kuma kwararru daga fagagen ilmomi mabambanta su yi mata taron dangi, wajen ba ta hakkinta kaman yanda ya kamata, sai dai duk da haka –kaman yanda ka’idar ilimin Fiqhu take cewa- abu mai sauki ba zai taba saraya ba saboda mai wahala- zan nemi taimako da dabarar Allah da karfinsa na ce:

Lallai siyaqin wannan ayar, da kuma halin da dangantakar ta kasance za su lizimta a tattaro wannan maulu’in da fuskoki hudu:

  • Fuska ta farko: mutuntaka, wadda ta zo daga kiran da Allah Madaukakin Sarki ya yi wa mutane a farkon ayar.
  • Fuska ta biyu: zamantakewa, wadda take bayyana a inda Allah ya fadi cewa “li’Ta’arafu”.
  • Fuska ta uku: bangaren ruhi, inda za mu ciro shi daga inda Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Inna akramakum indalLahi atkaakum”.
  • Fuska ta hudu: ta ilimi ne da sakafa, wadda za mu ciro shi daga inda Allah Madaukakin Sarki ya ce: “InnalLaha alimun khabir”.

Tarjama: 7 ga watan Ramadhan, 1438 = 2 ga watan Jun, 2017

Domin kallon video: https://www.youtube.com/watch?v=UX6WVh-oxDU&t=25s