0001 – Sakin Aure

0
3056

Tambaya

Assalamu alaikum, Malam
Idan mutum yasaki matarsa saki daya harta gama idda bai mayar da itaba sai aka sake daura musu aure, to malam meye matsayin wannan saki dayan yana nan ko babu wannan saki a tsakaninsu. Na gode.

Amsa

Daga Dr. Ibrahim Maqary: Qaulin kusan ilahirin malamai saki yana nan kuma igiya biyu ya rage mata ko da kuwa tayi aure a tsakanin sakin da maidawan.