0002 – Sallar Kasaru

0
4125

Tambaya

Aslm! Na kasance a NYSC camp amma mun shafa 21 days muna sallah qasaru bisa umurnin camp liman. Meye hukuncin?

Amsa

Daga Dr. Ibrahim Maqary: Mutumin da yake Camp a Fatawa mafi inganci ba zai yi Qasru ba, saboda kwanakin Qasru kwana Uku ne a wajen Malikiyah ko hudu a wajen Hanbaliyah, wasu sun dogara da Hadisin Ibn Abbas dake Bukhari da Muslim cewa Manzon Allah Yayi Qasru a makkah kwana sha bakwai, wannan babu hujjah a cikinsa domin idan mutum zai zauna wani abu ya tsareshi alhali kullum yana niyar tafiya sai wani abu ya riqa tasowa wanda zai jinkirta tafiyar babu komai yayi ta qasru don bashi da niyar zama wani dalili ke tsawaita zaman, amma yin Qasru fiye da kwana sha tara sam bai zo a hadisi ba ko a yanayin da muka ambata, wannan fatawa ce ta wasu daidaikun malamai wanda sun saba da ilahirin malaman musulunci, kuma babu hujja akan abinda suke yi.