0003 – Zato da Zancen Zuci

0
4299

Tambaya

Assalamu alaikum.
Malam inada tambayoyi Kamar haka, ta farkodai itace:. Malam nine nike naman wani aiki, Kuma Ina adduar kullum ALLAH yabani, kawai wataran hadu da wani abokina yake cemin kwana biu na boye kona samu aikin da nike nemane, sainace mai “da nasamu aikin kana ganina yanzu tare dakai, saikawai yacemin to tunda hkn Kar Allah yabani aikin don dai indinga zama tare dashing.

To Malam atakaicedai Allah baisa nasamu aikinnanba, tare da cika ka’idodi danayi, anma dika abokina sunsamu, haka Kuma din aikin da nanema sainaga Kamar zankama saiya kuccemin.

To Malam nayi kokarin hana zuciyata tinanin wannan mutun ko sanadiyarsa haka ke faruwa dani, anma na kasa, sbd sanin cewa kandun baka gskyn, sannan wani baimasan yanada Shiba. To mlm ya matsayin tauhidina? Kuma mezanyi don kaucewa wannan tinanin??

Tambaya ta biu Kuma itace :. Malam miye hukuncin zancen zuci? Sai mutun yayi tinanin zagin wani idan anfadi sunanshi, kokuma dai da amfadi abu ko miye ne tare da zahirin gskyr abun anma azuci Sai yace karyace???

Amsa

Daga Dr. Ibrahim Maqary: Da Tambaya ta farko da ta biyu duk zunubai ne na zuciya da ya dace Mumini ya guje masu, mun sani Allah Taala Yana fada (qul lan yusibana illa ma katabalalLahu lana…) ana so Mumini ya sakankance babu abinda zai faru dashi sai abinda Allah Ya rubuta masa.

Game da niyyar zuciya kuma matuqar ba a aikata abin ba in Allah Ya yarda yafaffe ne, domin wannan rashin aikatawar ma yana nuna qarfin imani ne, amma a barayi daya kuma akwai laifukan da dama na zuciya ne, kamar qudurta so ko qi, gaskatawa ko qaryatawa, mafi kyau gareka duk abinda baka san gaskiyansa ko qaryansa ba ka fawwala lamarinsa ga Allah, kada ka karba har sai ka san hujjar karban.

SHARE
Previous article0002 – Sallar Kasaru
Next articleSufism