ZAKKAR FID DA KAI A TAQAICE…

0
1299

 

ZAKKAR FID- DA KAI

“Zakkatul Fidir” ita ce ake kira a Hausance da “Zakkar Fid da kai”, ko “Zakkar kono”, ma’anarta kuma ita ce: zakkar da ta wajaba kowane Musulmi ya fitar da ita kafin gabatar da sallar Idi ƙarama, kowa gwargwadon sa’i ɗaya na abincin da aka fi amfani da shi a garin da yake, ba babba, ba yaro, ba namiji ba mace, ba ɗa ba bawa; kowa sai ya fitar; Sayyiduna Abdullahi Ibn Umar (Allah ya ƙara yarda da su) ya ruwaito cewa: “Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa Alihi wa sallam) ya farlanta wa mutane bayar da zakkar fid da kai a watan Ramadhan, sa’i ne na dabino, ko na alkama, da ta wajaba akan kowane Musulmi, ɗa ko bawa, namiji ko mace.” [al-Bukhari, 2/130; Muslim, 2/677].. kowa zai fitar wa wanda ciyar da shi ta wajaba akansa..

Amma sharaɗin bayar da ita shi ne ya zamana mutum yana mallakar sama da abin da yake buƙata a ranar idi, saboda haka talakan da ba ya mallakan sama da abin da zai ci, shi da iyalansa a daren idi, wato daren da aka ga watan Shawwal, da kuma ranar idi, to kuwa lallai wannan ibada ta zakkar fid da kai ba ta hau kansa ba, saboda ba zai iya ba, shi kuwa: ((Allah ba ya ɗaura wa kowane rai wani abu sai abin da zai iya)) [al-Bakra: 286]..

Allah Maɗaukakin Sarki ya farlanta wannan zakka ne domin ta tsarkake mai Azumi daga kura-kuren da ya aikata a lokacin Azumi, irin su: alfasha a zance, da kuma ayyuka marasa fa’ida.. haka kuma Allah Maɗaukakin Sarki ya farlanta zakkar fid da kai ne; saboda a wadata mabuƙata, kada a bari har sai sun roƙi abin da za su ci a ranar idi, ranar da gaba ɗayan Musulmai suke cike da farin ciki da zuwansa, a dalilin haka ne ma Sayyiduna RasululLahi (SallalLahu alaiHi wa Alihi wa sallam) yake cewa: ((Ku hutar da su yawon nema a wannan rana)) [Dar Kutniy 2/152; al-Baihakiy, 4/175].

Game da lokacin da ake fitar da zakkar fid da kai kuwa, malamai sun ƙara wa juna sani, inda bayanansu game da haka ya zo kaman haka:

• Mazhabar Imam Abu Hanifah (Allah ya ƙara yarda da shi): ta tafi akan cewa za a fitar zakkar fid da kai ne da zaran alfijir din ranar idin ƙaramar sallah ya fito.

• Mazhabar Imam as-Shafi’iy, da Mazhabar Imam Ahmad (Allah ya ƙara yarda da su): sun tafi akan cewa zakkar fid da kai tana wajaba ne da zaran rana ta faɗa a ranar ƙarshe na watan Ramadhan..

• Mazhabar Imam Malik (Allah ya ƙara yarda da shi): su kuwa Malikawa suna ganin cewa ya halatta a fitar da zakkar fid da kai kafin ranar idi da kwana ɗaya ko biyu; domin an ruwaito cewa Sayyiduna Abdullah bn Umar da Al-Hassan (Allah ya ƙara yarda da su) cewa babu laifi a fitar da wannan zakkar kafin ranar idi da kwana ɗaya ko biyu…

Saboda haka sam babu laifi idan aka gaggauta bayar da zakkar tun kafin ranar idin da kwana ɗaya ko biyu..

Sai dai fa idan lokacin bayar da wannan zakka ya wuce, to zakkar ba ta saraya, dole ne a bayar da ita a matsayin biyan bashi “Ƙadha’i”.

Ana bayar da wannan zakka ne ga talakawa, haka ma mutane takwas ɗin da ake ba su zakka –kaman yanda ya zo a ayar Suratut Tauba- suna cikin waɗanda za a bai wa wannan zakkar ta fid da kai, Allah Maɗaukakin Sarki yana cewa: ((Ita zakka ana bayar da ita ne ga talakawa faƙirai, da talakawa miskinai, da masu aikin tattara ta, da kuma waɗanda ake tarairayar zukatansu domin shiga Musulunci, da wurin ƴanta bayi, da biyan bashin wanda bashi ya yi masu kanta, da mayaƙa masu ɗaukaka kalmar Allah, da matafiya, wannan kam wajibi ne da ya zo daga Allah, lallai Allah shi ne cikakken masani, mai kuma yawan hikima)) [at-Tauba: 60].

Sai dai duk da haka, za a iya bai wa mutum ɗaya, kaman yanda za a iya rarrabawa mutane sama da ɗaya, abin dai da za a lura da shi kawai shi ne: hutar da mabuƙata da wahalar nema a wannan rana..

Kaman yanda muka bayyana a baya, ana fitar da zakkar fid da kai ne daga abincin da aka fi amfani da shi a garin da mutum yake, kaman mu ce: shinkafa, da masara, da dawa da sauransu, kowane mutum za a fitar masa da sa’i ɗaya ne irin sa’in Sayyiduna RasululLah (SallalLahu alaiHi wa Alihi wa sallam), wanda ya yi daidai da (kilo giram 2.04); amma wanda ya bayar da abin da yafi haka ya kyauta, zai kuma sami lada akan hakan in Allah ya yarda.

Haka ma za a iya fitar da zakkar fid da kai da kuɗi, sai a kiyasta kuɗin abincin da za a fitar ɗin a bai wa mabuƙata..

Allah ya amshi ibadunmu, ya kuma dawwamar mana da darasin da muka ɗauka a cikin wannan mata, ta yanda za mu cigaba da gabatar da ayyukan alhairi na ibada, da na mu’amala a tsakaninmu, mu cigaba da kyautata wa juna, da kuma hararo kwarjinin Allah Maɗaukakin Sarki a dukan rayuwarmu, amin.

Saleh Kaura